Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Tinubu Ya Yabawa Super Eagles Duk Da Rashin Nasarar Da Ta Yi

41

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yabawa Super Eagles bisa kwazon da suka nuna a fafatawar da suka yi na samun tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA, duk da rashin nasarar da kungiyar ta yi a wasan daf da na karshe na ranar Lahadi.

A cikin wani sako da mai magana da  yawun shugaban kasar, Mista Bayo Onanuga ya fitar a ranar Litinin Da ya gabata yayin da yake jawabi ga sakamakon, shugaba Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya da su amince da kokarin ‘yan wasan tare da ci gaba da marawa kungiyar ta kasa baya.

Ya kuma baiwa Eagles kwarin guiwa da su mayar da su baya wajen rashin nasara a hannun jamhuriyar dimokaradiyyar Congo da kuma shirye-shiryen tunkarar gasar cin kofin Afrika da za a yi daga watan Disamba na 2025 zuwa Janairu 2026 a Morocco.

Shugaba Tinubu ya ce; “Mafarkin Najeriya na shiga gasar cin kofin duniya ya ruguje yayin da Congo DR ta fitar da Super Eagles a wasan share fage na neman cancantar shiga gasar a daren Lahadi a Morocco.

“Duk da rashin jin daɗi, dole ne mu yaba wa ‘yan wasan saboda ƙoƙarin da suka yi kuma mu ci gaba da tallafa musu.”

Ya kuma kara jaddada bukatar daukar matakin gyara cikin gaggawa don karfafa tsarin wasan kwallon kafa na Najeriya gabanin wasannin kasa da kasa a nan gaba.

“Yanzu dole ne mu toshe dukkan madogara. Masu kula da kwallon kafa, ‘yan wasanmu, da kuma duk masu ruwa da tsaki dole ne su koma kan hukumar zana,” in ji shi.

Shugaba Tinubu ya sake tabbatar da cewa idan aka sabunta mayar da hankali, da’a, da kuma tsari mai kyau, wasan kwallon kafa na Najeriya zai iya dawo da matsayinsa a matsayin mai karfi a fagen Afirka da duniya.

“Ko da yake yana da zafi cewa Eagles sun kasa samun tikitin shiga gasar cin kofin duniya karo na biyu a jere, dole ne a yaba wa kungiyar bisa kokarin da ta yi wajen kaiwa ga Mundial, musamman bayan da suka yi nasara a wasansu na farko a gasar.

“Duk da rashin jin dadin da aka samu, dole ne mu yaba wa ‘yan wasan saboda kokarin da suka yi kuma mu ci gaba da tallafa musu.

“Yanzu dole ne mu toshe dukkan madogara, masu kula da wasan kwallon kafa, ‘yan wasa, da kuma duk masu ruwa da tsaki dole ne su koma kan allon zane.

“Yanzu ne lokacin da za a mayar da hankali ga duk kokarin da ake yi a gasar cin kofin duniya. Dole ne Super Eagles mu dawo da daukakar da aka rasa,” in ji Shugaba Tinubu.

Eagles ta yi rashin nasara a bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan an tashi wasan da ci 1-1 a karin lokaci. DR Congo ta samu nasara da ci 4-3 a bugun fenareti, inda ta tsallake zuwa wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta 2026.

 

Aisha. Yahaya, Lagos

 

Comments are closed.